Shugaba Bola Tinubu ya sake nada Malam Mele Kyari a matsayin babban jami’in gudanarwa na kamfanin man fetur na kasa (NNPCL).

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale, ya fitar a ranar Litinin.
A cewar Ngelale, nadin zai fara aiki ne daga ranar Juma’a 1 ga Disamba, 2023.

Ya ce shugaban ya kuma nada shugaban kwamitin gudanarwa na kamfanin, tare da Cif Pius Akinyelure.

Ya ce, a bisa bin sashe na 59 (2) na dokar masana’antar man fetur ta shekarar 2021, shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da nadin sabon kwamitin gudanarwa na kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) daga ranar 1 ga Disamba, 2023.