Gwamnan Jihar Akwa Ibom Umo Eno ya daura damarar korar duk wani shugaban karamar hukumar a Jihar da ya daina zama a yankinsa.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a gurin bikin rantsar da gwamnatin rikon kwarya ta kananan hukumomi 31 na Jihar, a gidan gwamnatin Jihar da ke Uyo.
Bayan bayyana kudirin da gwamnan ya gabatar a gaban majalisar dokokin Jihar ta amince da bukatar gwamnan na nada gwamnatin rikon kwarya a kananan hukumomi, bayan karewar wa’adin shugaban kananan hukumomin.

Da ya ke jawabi bayan kammala rantsar da shugaban kananan hukumomin, gwamnan ya tabbatar da matsayarsa akan cewa ya zama wajibi su zauna a yankunan nasu.

Gwamnan ya ce ba zai yiwu shugabannin kananan hukumomin su shugabanci yankunansu daga wani gurin ba.
Gwamnan ya kara da cewa matukar ya gano wanda yake mulkar yankinsa daga wani gurin zai sauke shi daga kan mukaminsa.
Daga karshe ya bayyana cewa dukkan wanda ba zai iya zama a yankinsa ba ya rubuta takardar murabus.