Gwamnatin jihar Zamfara ta ware Naira biliyan 1.95 a cikin kasafin kudin shekarar 2024 domin sake gina fadar sarakunan jihar 18.

Kwamishinan al’amuran kananan hukumomi da masarautu na jihar Alhaji Ahmad Yandi ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a Gusau.
Yandi wanda ya bayyana a gaban zama na musamman na kwamitin kudi da kasafin kudi na majalisar ya ce aikin zai kara daukaka martabar sarakunan gargajiya.

A halin yanzu, Gwamna Dauda Lawal a ranar Alhamis ya gabatar da kasafin kudin jihar na Naira biliyan 423.5 ga majalisar dokoki domin amincewa.

Yandi wanda ya bayyana a gaban kwamitin don kare kasafin kudin ma’aikatarsa, ya ce yana daga cikin manufofin gwamnati inganta martabar cibiyar gargajiya a jihar.
Ya kara da cewa, sauran ayyukan da za a aiwatar a cikin kasafin kudin sun hada da fadada harabar ma’aikatar, da ofishin hukumar kula da ayyukan kananan hukumomi da sauransu.
A nasa bangaren, babban sakataren ma’aikatar ayyuka da samar da ababen more rayuwa, Alhaji Shehu Baraya, ya ce an ware sama da Naira biliyan 140 domin gudanar da ayyukan tituna da sauran ababen more rayuwa a jihar.