Wata ɗaliba ƴar shekara 18 da haihuwa a Kwalejin Kiwon Lafiya ta jihar Neja da ke Kontagora, Zubaida Sanusi, na tsare a hannun ƴan sanda.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ana zargin Zubaida ne bisa yin aiki a matsayin mai ba da bayanai ga ƴan bindiga.
Kwamishinan ƴan sandan jihar, Shawulu Ebenezer Danmamman, ya bayyana cewa an kama ɗalibar ne biyo bayan kama wani ɗan bindiga mai suna Umar Aliyu, wanda aka fi sani da Babuga Datijo mai shekaru 37.

Ya ce yayin bincike an gano lambar ɗaya daga cikin ƴan bindigan da ake nema ruwa a jallo, Shaibu Haruna a cikin wayar ɗalibar, inda aka ajiye lambar.

Ya ce ɗalibar ta amsa cewa wata mata mai suna Aisha Mohammed ce ta gabatar da ita ga Shaibu, inda ta ƙara da cewa Shaibu ya kan bata kuɗi domin yin lalata da ita.
Kwamishinan ƴan sandan ya ce ƙoƙarin da aka yi na cafke wasu ƴan kungiyar ta Aliyu, ya sa aka gano wata lambar waya a Kontagora mallakar ɗalibar da ake zargin.
Ya ce shugaban ƙungiyar ya bayar da lambobin wayar wasu ƴan ƙungiyar guda biyu Maidabo da Shaibu Haruna na garin Garatu, ƙaramar hukumar Bosso.
Ya ce an kama wani Motse Mohammed mai shekaru 47 da Aliya Mohammed mai shekaru 48, mazauna garin Salka, ƙaramar hukumar Magama da laifin tuntubar ƴan bindigar tare da zama masu ba da bayanai a wasu hare-hare.
Ya ce rundunar ƴan sandan ta tabbatar da cewa ƴan bindigan sun aike da naira dubu 10 ga mutanen biyu ta hanyar wani POS a garin Salka.