Tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau ya tofa albarkacin bakinsa game da shari’ar zaben da ake yi a kotun koli.

A wata zantawa da aka yi da shi, Sanata Ibrahim Shekarau ya ba gwamna Abba Kabir Yusuf da Nasiru Yusuf Gawuna shawara.

Babban ‘dan siyasar ya yi kira ga gwamna mai-ci da Nasiru Yusuf Gawuna da kotu ta ce shi ya lashe zabe da su koma Allah SWT.

Malam Shekarau ya bukaci ‘yan siyasar su roki zabin Ubangiji kuma su karbi duk kaddarar da ta auka masu bayan hukuncin kotu.

Rohoton na zuwa ne a daidai lokacin da ake jiran kotun koli ta yi hukunci karshe a shari’ar zaben gwamnan na jihar Kano.

Tsohon Ministan ilmin ya yi magana a Rumfar Afrika, ya ce abin da ya fi dacewa shi ne ayi addu’ar zabi mafi alheri ga mutanen Kano.

Shekarau wanda ya yi gwamna tsakanin shekarar 2003 da 2011 ya yi wannan addu’ar, sannan ya ce yana fatan APC da NNPP za su yi irin haka.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: