Hukumar yaƙi da hana sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA a jihar Kaduna, ta ce ta kama haramtattun kaya guda 1,458,709 a watan Disamba.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in yada labarai na hukumar Shuaibu Omale ya raba wa kamfanin manema labarai a Kaduna ranar Talata.
Omale ya ce haramtattun kwayoyi da aka kama sun hada da hodar iblis, tabar wiwi, tramadol, methamphetamine da sauran abubuwan da suka shafi kwakwalwa.

Haka zalika, kakakin ya ce rundunar ta kama mutane 103 da ake zargi, da ke wakiltar masu safarar miyagun kwayoyi, dillalai da masu shan muggan kwayoyi.

Olame ya kara da cewa rundunar ta gudanar da shirye-shiryen wayar da kan jama’a da dama a fadin jihar da nufin wayar da kan ‘yan kasa kan illolin da ke tattare da shan muggan kwayoyi da safarar miyagun kwayoyi.
Sannan sun wargaza gidajen haramtattun kwayoyi guda 26 yayin da rundunar ta kama wasu laifuka shida tare da gurfanar da mutane 24 da ake tuhuma a cikin watan Disamba na shekarar 2023.