Jam’iyyar APC da gwamnatin jihar Kano sun yi musayar yawu kan zargin wani shiri na karkatar da sama da Naira biliyan Takwas na kuɗin ƙananan hukumomin jihar.

Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas, a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a Abuja, ya yi zargin cewa gwamnatin jihar na ƙoƙarin karkatar da naira biliyan 8,080,190,875.13.
A cewarsa rashin tabbas kan abin da zai kasance sakamakon hukuncin da kotun ƙoli ta yanke kan zaɓen gwamnan jihar ya sanya gwamnatin ɗaukar wannan matakin.

Shugaban jam’iyyar APC ya kuma gargadi ƙananan hukumomi da bankunan kasuwanci da su dakatar da shirin fitar da kuɗaɗen.

Jaridar Daily Trust ta ce da yake mayar da martani, kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano, Baba Halilu Dantiye, ya bayyana cewa.
Sannen abu ne cewa gwamnatin jihar Kano a ƙarƙashin ingantaccen shugabancin Injiniya Abba Kabir Yusuf, a cikin watanni bakwai da suka gabata ta yi suna wajen ganin an tabbatar da gaskiya da adalci da amfani da dukiyar al’umma yadda ya dace.
Ya kara da cewa gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ba za ta bari mutanen da ke jin zafi ba domin faɗuwa zaɓe kaɗai ba, amma saboda sun yi asarar hanyoyin satar dukiyar gwamnati su ɗauke mata hankali ba.