Gwamnatin jihar Zamfara ta sake rufe kasuwannin shanu 11 a wasu sassan jihar har sai baba ta gani.

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Munnir Haidara, ya ce an rufe kasuwannin ne sakamakon rahotannin tsaro cewa ƴan bindiga na amfani da su wajen sayar da shanun sata.
Kasuwannin da abin ya shafa a cewar Haidara, su ne kasuwannin Tsafe da Bilbis da ke ƙaramar hukumar Tsafe, kasuwar Jangebe dake ƙaramar hukumar Talata-Mafara da kasuwar Wuya dake ƙaramar hukumar Anka.

Sauran sune kasuwar Magamin Diddi da ke ƙaramar hukumar Maradun, kasuwar Galadi a ƙaramar hukumar Shinkafi, kasuwar Mada a ƙaramar hukumar Gusau, da kasuwar Sabon Birnin Dan Ali dake ƙaramar hukumar Birnin Magaji.

Sannan akwai kasuwar Kokiya, Chigama da Nasarawar Godel duk a ƙaramar hukumar Birnin Magaji.
Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar ta umurci jami’an tsaro da su tabbatar da bin doka da oda tare da kama duk wanda ya karya dokar.