Wata kotu a Jihar Kano ta tisa keyar wata matar auren da ake zargi da kisan abokin kasuwancin ta a gidanta mai suna Nafiu Hafiz Gorondo zuwa gidan yari.

An gurfanar da matar a gaban Babar Kotun Majistare da ke zamanta a Yankaba bisa zargin ta da caccaka wa marigayin wuka lamarin da ya yi sanadiyyar rasuwarsa.

Mai gabatar da kara kuma lauyan gwamnatin jihar, Barista Lamido Sorondinki ya shaida wa kotun cewa ana tuhumar matar da laifuka biyu na kokarin kashe kanta da kuma yi wa wani kisan gilla, laifukan da suka saba da sashe na 281 da na 221 na Kundin manyan laiduka.

A cewar Barista Lamido Sorondinki wadda ake zargin ta yi amfani da wuka mai kaifi don kashe kanta inda ta yanke hannunta na hagu.

Ya ce a lokacin ne ta yi amfani da wannan wukar ta caka wa Nafiu Hafizu a kahon zuciya, lamarin da ya yi sanadiyyar rasuwarsa.

Wadda ake zargin ta amsa aikata laifi na farko yayin da ta musanta aikata laifi na biyu.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Hadiza Abdurrahman ta bayar da umarnin tsare wadanda ake zargi a gidan gyaran hali tare da dage shari’ar zuwa ranar 1 ga watan Fabrairu, 2024.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: