Kotun shari’ar Musulunci da ke jihar Kano ta umarci tsare wani matashin kan zargin karar da dattawan Unguwansu su ka yi a kansa.

Wanda ake zargin mai suna Musa Okashatu Gobirawa ya yi barazanar hallaka wasu dattawa a Unguwansu da ya ke zargin za su kwace filinsa.
Kotun ta umarci tsare shi a gidan kaso inda ta ce aikata hakan ya sabawa sashe na 227 na kundin laifuka da hukuncin Shari’ar Musulunci.

An kama wanda ake zargin ne bayan wani Muhammad Sani Hussain da Bashir Namoriki su kaa shigar da kara a gaban kotun.

Wanda ake zargin ya yi barazanar ne bayan mambobin kwamitin Unguwar sun yi zama inda suka kawo wata doka wacce ba ta masa dadi ba.
Har ila yau, wanda ake zargin ya amince da furta kalaman yayin da mai gabatar da kara, Aliyu Abidin Murtala ya karanto masa laifukan.
Ya ce ya fusata ne bayan mambobin kwamitin sun yi kokarin kwace masa filinsa inda suka ce ba na shi ba ne.
Mai Shari’a, Mallam Nura Yusuf ya umarci tsare matashin tare da dage sauraran karar zuwa ranar 11 ga watan Janairun 2024.