Bankin duniya ya ce rayuwa za ta kara tsanani kuma akwai yiwuwar kashe-kashe su yawaita musamman a wasu jihohin Arewa.

Jaridar Punch ta ruwaito babban bankin na duniya yana cewa za ayi ta fama da wadannan matsaloli har zuwa watan Mayu na shekarar 2024.

Jihohin da abin zai iya shafa sosai sun hada da Borno, Kaduna, Katsina, Sokoto sai kuma Zamfara da wasu bangarori a Adamawa.

Rahoton da bankin ya fito ya nuna ana fuskantar matsala wajen noma a kasar, hakan zai yi tasiri wajen amfanin gona da za a samu.

Adadin kayan amfanin da za a samu a kakar 2023/2024 zai ragu da 2% idan aka kwatanta da albarkar noman shekarun baya.

Matsalolin da aka samu a Najeriya za su taimaka wajen raguwar kayan abinci a nahiyar Afrika kamar yadda aka fitar a rahoton.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: