Rundunar Operation safe haven reshen Jihar Filato na musanta Kama kwamandan rundunar ta na karamar hukumar Bokkos a Jihar.

 

Mai magana da yawun rundunar Kyaftin James Oya ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwar da ya fitar.

 

Rundunar ta bayyana cewa ana yada rahotan cewa ana zargin kwamandan da hannu a hallaka mutane sama da 100 da ‘yan bindiga suka yi a kananan hukumomin Bokkos Barikin-Ladi da Mungu a Jihar.

 

Rundunar ta bukaci mutane su yi watsi da rahotan wanda bashi da tushe ballantana makama.

 

Sanarwar ta kara da cewa an yi hakan ne domin a batawa rundunar suna a idon duniya.

 

Idan ba a manta ba, wasu da ba a san ko su waye ba sun kai wasu hare-hare a ƙananan hukumomin Bokkos da Barinkin Ladi a jihar Filato.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: