Gwamnatin jihar Zamfara ta hamtawa masu riƙe da sarautar gargajiya bayar da izinin hakar ma’adinai a jihar baki ɗaya.

Gwamna Dauda Lawal Dare ne ya sanya hannu tare da bayar daa umarnin hanin a yayin zaman majalisar zartarwa da ya wakana yau Alhamis.


Cikin wata sanarwa da mia magana da yawun gwamnan Sulaiman Bala Idris ya sanya wa hannu, ya ce dakatarwar n adaga matakin daƙile ayyukan ta’addanci a jihar.
Dokar ta haramtawa masu riƙe da sarautar gargajiya bayar da izinin harkar ma’adanai ga daidaikun mutane, kamfanoni da kungiyoyi.
Wannan dai wani mataki ne da gwamnatin ta ɗauka a ƙoƙarin ganin an daƙile ayyukan masu garkuwa, kisan gilla da sauran ayyukan ta’addanci.
