Hukumar dake Kula da aikin hajji a Najeriya ta bayyana kudin kujerar aikin hajjjn bana a naira miliyan hudu da 900.

Hukumar NAHCON a Najeriya mai Kula da aikin hajji ta ce maniyyata za su biya kudi har kusan miliyan biyar.


Kamar yadda matashiya TV bahaushiyar Tasha Mai tsage gaskiya komai dacinta ta kawo muku labarin ragin kudin da kasar Saudiyya ta yi na aikin hajjin bana a farkon mako.
Saudiyya ta yi ragin kudi tsakanin abubuwan da shuka shafi tikiti sufuri da masauki.
Sai dai a bayaninta hukumar ta bakin mataimakiyar Darktar hukumar Fatima Sanda Usara ta ce kudin ya kasance naira miliyan hudu 900 duk da ragin da aka yi.
A kwanakin baya sai da hukumar ta bayyana cewa dukkan maniyyaci ya ajiye naira miliyan hudu da rabi na aikin hajjin bana.
Sannan masu sharhi suka dinga bayyana cewa kudin zai iya kai wa miliyan biyar kafin lokacin.
Da take jawabi Fatima Sanda ta ce maniyyata su gaggauta biyan miliyan hudu da 900, zuwa 12 ga watan Fabarairu kafin rufewa 29 ga wata.
Sai dai ko a kwanakin baya da hukumar ta ce miliyan hudu da rabi wasu bu su iya biya ba.
Hakan dai na da alaka da yadda darajar kudin Najeriya ke kara faduwa.