Rundunar ƴan sanda a jihar Legas sun kamaa mutane 43 a wani samame da su ka kai cikin dare.



An kai suamen ne a yankin Oshodi daa kewaye.
Hakan na kunshe aa wata sanarwa da rundunar ta fitar a shafinta na X a yau.
A cikin sanarwar, sun ce sun kai harin ne a ranar Talata da daddare a wuraren wasannin dare har su ka samu nasarar kwato wata bindiga kirar pistol.
Samamen da su ka kai na zuwa ne bayan da su ka samu kwararan bayanai a kan wuraren wasanni da kuma mutanen da ke zuwa wajen.
Rundunar ta ce za ta miƙa waɗanda ta kama a gaban kotu domin girbar abinda su ka shuka.
