Hukumomi a jihar Katsina sun garkame wasu gidajen mai uku bisa zargin sayarwa ƴan bindiga man fetur.

Kwamitin kartakwana kan saro da inganta abinci a jihar ya kuma cafke wasu mutane 10 da ake zargin suna da hannu cikin kasuwancin man fetur ɗin da ƴan bindigar.


Channels tv ta ruwaito Shugaban Kwamitin, Jabiru Tsauri a ranar Litinin ya ce an zurfafa bincike kafin ɗaukar mataki.
Jabiru Tsauri, ya kara da cewa bayan laifin bawa ‘yan ta’adda man fetur da ake zargin gidajen man da aikatawa, ana kuma tuhumarsu da sayar da man bisa farashi mai tsada.
Ya ce gidajen sun sayar da man sun sayar da litar mai a kan ₦733, ₦715 da kuma ₦730 wanda ya haura farashin da hukuma ta ƙayyade.