Kwamitin bincike da gwamnatin jihar Kano ta kafa ya bayyana matakin da zai dauka kan zargin badakalar da tsohon gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya yi.

Kwamitin ya ce zai sake duba kan kadarorin da aka siyar da kuma karkatar da su ga wasu tsiraru na gwamnatin da ta gabata.

Shugaban kwamitin, Mai Shari’a, Farouk Adamu shi ya bayyana haka a jiya Litinin 29 ga watan Afrilu a Kano.

Farouk ya ce daga cikin aikin kwamitin shi ne sake duba kan siyar da filayen idi da wuraren tarihi da gidaje da kuma makabartu a birnin mallakin gwamnatin jihar.

Ya ce za su yi bincike ko akwai almundahana yayin gudanar da su da kuma hukunta waɗanda ke da hannu a ciki.

Har ila yau, Farouk ya ce ba a kafa kwamitin domin bita-da-kulli kan wani ba illa binciken gaskiya.

Alkalin ya ba da tabbaci ga al’umma cewa zai yi adalci yayin binciken Ganduje ba tare da nuna bambanci ba da sauran wadanda abin ya shafa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: