Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya bayyana aniyarsa ta yin hadaka da kasar Hungary a fannin tsaro da noma.

A cewar ministan, yunkurin da suka yi yana daga cikin bada muhimmanci da gwamnatin Bola Tinubu ta yi wurin samar da cikakken tsaro a Abuja.


Mista Wike ya bayyana kudurin ne yayin wata ziyara da ya kai ofishin jakadancin kasar Hungary dake Abuja.
A lokacin ziyarar, ministan ya bayyana abubuwan da gwamnatin ke buƙata daga kasar Hungary domin dakile barazanar tsaro a Abuja.
Ya lissafa bukatar samun jirage marasa matuka da za su rika samar da cikakken tsaro a birnin tarayyar.
Amma sai dai ya ce akwai bukatar a tantance irin jiragen da za su dace da birnin domin kaucewa ɓacin rana da kuma kasancewarsu ingantattu.
Mista Wike ya kara da cewa lalle akwai matsalar tsaro a Abuja amma da yardar Allah za su magance ta idan suka samu hadakar.