Yan bindiga sun sake kai mummunan hari a karamar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.

 

Maharan sun hallaka mutane da dama a Kakangi da Unguwar Matinja a ranar Alhamis 2 ga watan Mayu.

 

Wannan hari na zuwa ne mako daya bayan miyagu sun hallaka wasu mutane uku a Kakangi da ke jihar.

 

Yayin harin, maharan sun hallaka yan banga guda takwas tare da sace masu sarautar gargajiya na Kakangi da Kisaya.

 

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mansir Hasssan ya tabbatar da haka ga gidan talabijin na Channels.

 

Mansir ya ce jami’ansu suna ci gaba da tattara bayanai domin sanin yawan wadanda suka mutu.

 

Wani shugaban a yankin, Muhammad Amin ya ce maharan sun farmaki ‘yan bangan ne lokacin da suke neman ceto wasu da aka yi garkuwa da su.

 

Amin ya ce an yi garkuwa da mutanen ne yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa jana’iza a Kakangi da Sabon Layi.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: