Kungiyar dillalan tumatur ta Najeriya da hadaddiyar kungiyar dillalan kayan abinci da shanu ta Najeriya sun yi barazanar rage kai tumatur jihar Legas saboda lalata musu dukiya da ake.

 

Shugaban kungiyar dillalan tumatur na kasa, Alhaji Ahmed Alaramma ne ya yi wannan barazanar a taron manema labarai a Zariya, jihar Kaduna a ranar Lahadi.

 

Ya ce lamarin da ya faru a kasuwar Oke-Odo da ke Legas, ya kai ga lalata kwandunan tumatur sama da 60,000 da babu kowa aciki.

 

Alaramma ya bayyana cewa, an fara amfani da kwandunan ne wajen kai tumatur zuwa Kudancin.

 

Ya ce sama da mambobin kungiyar 70 ne ke ba da hayar kwandunan ga dillalan tumatur a fadin kasar nan, suna da akwatuna sama da 60,000 da ake shirin mayar da su Arewa a kasuwa a lokacin da rikicin ya tashi.

 

A cewarsa, kowane holokon kwando ya kai Naira 6000, don haka mambobin kungiyar sun yi asarar jarin sama da miliyan 360.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: