Gwamnatin Tarayya za ta rage yawan jami’an tsaro da ke binciken kayayyaki a filayen jiragen sama.

Hukumar kula da jiragen sama ta FAAN da ofishin mai ba Bola Tinubu shawara kan harkokin tsaro domin tabbatar da haka.


Hukumar ta ce za ta rage yawan jami’an ne daga hukumomi daban-daban a filayen jiragen saman.
FAAN ta ce ta dauki matakin ne domin saukaka tafiye-tafiye yayin da fasinjoji ke kokawa kan yawan binciken a filayen jiragen saman Najeriya.
Babbar manajan hukumar, Olubunmi Kuku ita ta bayyana haka a jiya Asabar 4 ga watan Mayu a Legas.
Kuku ta ce sun yi haɗaka da ofishin NSA domin rage yawan binciken da ake yi a filayen jiragen sama.
Babbar manajan ta ce za su yi haɗaka wurin amfani da na’urar CCTV a ofis domin tabbatar da ingancin aikinsu.
Har ila yau, Kuku ta ce sun yi magana da Nuhu Ribadu domin ganin an dakile matsalar da ta addabi matafiya.