
Kakakin majalissar jihar Edo Rt.Hon Blessing Agbebaku ya dakatar da yan majalissu guda uku a ranar Litinin akan zargin shirya manakisar cire shi tare da wasu manyan shuwaganni a majalissar.
Dakatattun yan majalissar sun hada da Mr Donald Okogbe Dan majalissa mai wakiltar Akoko-Edo 11, Bright Iyamu Dan majalissa mai wakiltar Orihonmwon ta kudu, da kuma Adeh Isibor Dan majalissa mai wakiltar Esan ta Arewa maso Gabas

A dawowa zaman majalissa a ranar Litinin, Agbebaku ya zargi dakatattun yan majalissun da cewar ana rudar su ne domin haddasa rikici tare da cire shugabancin majalissar.

Ya kuma zargi wasu mutane da kawo yan tsibbu cikin majalissar a daren Laraba 1 May, 2024 domin yin tsibbace-tsibbace tare da ajiye wasu layu a farfajiyar majalissar.
A kokarin su na mayar da amsa, yan majalissun da aka dakatar sun ce shugaban bashi da ikon dakatar da wani mamba na majalissar, dole sai ya sa anyi zabe kuma ya kyale mambobin su yi zaben.