Wani tsagin jam’iyyar NNPP ya kai ƙarar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen 2023, Rabi’u Musa Kwankwaso, da wasu mutane 13 a hukumar EFCC. Tsagin na NNPP ya kai ƙarar Kwankwaso gaban hukumar yaƙi da cin hancin ne bisa zargin karkatar da sama da biliyan 2.

Tsagin na NNPP a cikin ƙarar wacce sakatarenta na ƙasa, Oginni Olaposi, ya shigar ya yi zargin cewa an yi garkuwa sama da faɗi da kuɗaɗen asusun jam’iyyar.


Oginni Olaposi a cikin ƙarar wacce ya aike ga shugaban EFCC, ya ce kusan aƙalla N2.5bn da aka samu daga siyar da fom na takara da kuɗaɗen gudunmawa, shugabannin jam’iyyar da aka kora ba su ba da bayani a kansu ba.
Sakataren ya koka da cewa sama da faɗi da kuɗaɗen ya sanya ba a biya kuɗaɗen alawus na wakilan jam’iyyar ba da suka yi aiki a zaɓen 2023 a faɗin ƙasar nan.
Ya buƙaci hukumar EFCC da ta binciki asusun jam’iyyar NNPP tun daga watan Maris na 2022 har zuwa yanzu.
Sai dai da yake mayar da martani, kakakin kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na Kwankwaso, Ladipo Johnson, ya ce jam’iyyar ba ta da wani tsagi.
Ladipo ya haƙiƙance cewa wanda ba ɗan jam’iyya ba, ba shi da hurumin tambayar yadda aka kashe kuɗaɗen jam’iyyar.