Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano ya dora tubalin ginin titin saman da kudinsa ya kai Naira Biliyan 15 a wuraren Kofar ‘Dan Agundi a kwaryar birnin Kano.

Gwamnati ta bawa kamfanin CCG Nigeria Limited kwangilar aikin da ake sa ran kammalawa cikin watanni goma sha takwas domin rage cunkoson ababen hawa a yankunan.


A sakon da Sanusi Bature Dawakin Tofa, babban daraktan yada labaran gwamnan ya wallafa a shafinsa na Facebook, kammala titin zai kawo ci gaba a jihar Kano.
Yayin kaddamar da aikin titin mai hawa uku, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jaddada cewa gwamnatinsa na ayyukan raya kasa a fatansa na mayar da Kano babban birni.
Ya ce ya bayar da wasu kwangilolin manya-manyan titunan a Tal’udu a kokarin rage cunkoso.
A jawabinsa, Manajan ayyuka a kamfanin CCG Nigeria Limited, Mista Gee Wang ya yi alkawarin kammala aikin cikin watanni sha takwas din aka tsara tun da fari.