Gwmantin tarayya ta yi alkawarin dawo da wutar lantarki a kananan hukumomi guda takwas a Sokoto bayan shafe sama da shekaru 10 ba wuta.

 

Ƙananan hukumomin za su samu tagomashin ne bayan gwamnan jihar, Ahmed Aliyu, ya koka kan lamarin yayin da ya kai wa ministan makamashi, Adelabu Adebayo ziyara.

 

Rahoton da jaridar Daily Trust ta wallafa ya nuna cewa tuni an tura ma’aikata da za su gabatar da bincike domin dawo da wuta a yankunan.

 

A lokacin da yake jawabi a Sokoto, Mustafa Baba Umarah, jami’in ma’aikatar makamashi ta kasa ya ce za su bincika duk matsalolin da suke kananan hukumomin domin daukan mataki.

 

Jami’in ya ce gwamnati ta dukufa wurin tabbatar da cewa dukkan ‘yan Najeriya sun samu wutar lantarki.

 

Kwamishinan makamashi na jihar Sokoto, Sanusi Dan Fulani, ya ce kokarin da gwamnatin jihar ke yi wurin samar da wuta a kauyuka yana cikin alkawarin da gwamnan ya yi na inganta rayuwar mutanen karkara.

 

Kwamishinan ya ce samar da wuta a yankunan yana da muhimmanci sosai musamman wurin habaka tattalin arziki da noma.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: