A gobe Alhamis ne shugaban kasa Bola Tinubu zai kaddamar da tashar tsandauri a garin Funtua da ke Jihar Katsina.

 

Mataimakiyar daraktan yada labarai na hukumar kula da shige da ficen jiragen ruwa NSC ta Kasa Rebecca Adamu ce ta bayyana ta cikin wata sanarwa da ta fitar.

 

Rebecca ta ce kara kaddamar da tashar wata babbar nasara ce ta ci gaba da gwamnatin ta yi don habaka kasuwanci a kasar ta fuskoki da dama.

 

Sanarwar ta ce tashar tsandaurin ta Funtua za ta saukakawa masu shigo da kaya yankin Arewa da ba sa kusa da teku, sannan kuma za ta rage cunkuso a bakin tekun kasar da kuma samar da ayyukan yi da karin kudin shiga ga gwamnatocin kasar.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: