Shugaban jam’iyyar APC na Kasa Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bukaci masu hali da su taiimakawa iyalan wadanda suka mutu a harin masallaci da ya faru a garin Larabar Abasawa da ke Kano.

Shugaban jam’iyyar ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu a birnin tarayya Abuja a yau Asabar.

Dr ganduje ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke mika sako ta’aziyyarsa ga wadanda lamarin ya rutsa da su.
Shugaban ya ce taimakawa mutanen zai taimaka matuka wajen rage musu radadin halin da suka tsinci kansu a ciki.

Shugaban jam’iyyar ta APC ya kuma nuna damuwarsa dangane da faruwar lamarin tare da mika sakon jaje ga wadanda lamarin ya rutsa dasu da kuma addu’ar Allah ya bai’wa wanda ke kwance a asibiti lafiya.

Ganduje na wannan rokon ne bayan wani matashi mai suna Shafi’u Abubakar mai shekaru 38 a duniya ya sanyawa wasu masallata wuta a lokacin da suke tsaka da sallar a Asuba a garin Larabar Abasawa da ke cikin karamar hukumar Gezawa ta Jihar Kano wanda hakan ya yi sanadaiyyar mutuwar mutane 15 ya yin da, wasu ke kwance a asibitin Murtala da ke Kano.

Rahotanni sun bayyana cewa a lokacin da matshin ya sanya wuta a cikin masallacin mutane 32 ne a ciki ke yin sallah ,inda ya sanya musu wuta sakamakon wani sabani na rabon gad

Leave a Reply

%d bloggers like this: