Wata babbar kotun jihar Kano ta dakatar da dakatar da jami’an tsaron soji, DSS da ƴan sanda daga barin gidan sarki na Ƙofar Kudu bayan da sarkin Kano Muhammadu Sanusi ll ya shigar da ƙara.

Sannan kotun ta hana jami’an tsaro kama sarkin tare da masu naɗa sarki.
Kotun ƙarƙashin mai shari’a Amina Adamu Aliyu wanda ta bayar da umarnin a yau bayan da sarkin Kano Muhammadu Sanusi ll ya shigar da ƙara tare da wasu ƴan majalisar sarki guda hudu.

Wannan umarni na zuwa ne bayan da wata babbar kotun tarayya ta umarni jami’an tsaro su fitar da sarkin Kano malam Muhammadu Sanusi ll daga gidan sarki.

Sanna kotun ta yi umarni da jami’an tsaro au tabbatar sun kai Alhaji Aminu Ado Bayero fadarsa da ke Ƙofar Kudu.
Ana ta samun cin karo da umarnin kotu tun bayan rushe masarautu da majalisar dokokin jihar Kano ta yi a makon jiya.
Majalisar ta soke dokar da ta kafa masarautu biyar a Kano tare sa mayar da Muhammadu Sanusi ll a matsayin sarkin Kano.
Bayan turka turkar da ke faruwa, Alhaji Aminu Ado Bayero ya shigar da ƙara gaban wata kotun tarayya wanda ta yi umarni a mayar da shi fadarsa da ke Ƙofar Kudu.
Yayin da a gefe guda sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi ll ya shigar da ƙara ya na mai roƙo kotu ta hana aa kamashi sannan ta hana jami’an tsaro fita daga gidan.