Gwamnatin jihar Kano ta haramta duk wani taron jama’a da aka yi niyyar gudanar da zanga-zanga a cikin jihar.

 

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ranar Laraba.

 

Sanarwar ta ce gwamnan ya umarci ‘yan sanda, da hukumar kula da ayyukan gwamnati, da jami’an tsaron farin kaya na Najeriya da su kama su kuma tsare duk wani mutum ko kungiyar da ke gudanar da zanga-zanga a kan titunan jihar.

 

Bature ya ce matakin wani shiri ne na riga-kafi da nufin dakile duk wani abu da ka iya tabarbarewar doka da oda da makiya jihar suka shirya.

 

Bature ya kara da ce sun samu sahihin bayanan sirri da ke nuni da cewa wasu jiga-jigan jam’iyyar adawa a Kano sun tsara shirin daukar nauyin kungiyoyin dalibai da masu fafutukar siyasa daga wasu jihohin Arewa maso Yamma domin tada hargitsi da nufin cewa basa goyon bayan tsige Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero.

 

Gwamnatin jihar ta fito karara ta haramta zanga-zanga kowace iri ce, kuma za a kama mutanen da aka samu a kan titunan Kano suna irin wannan aika-aikar.

 

Gwamnatin ta bukaci daukacin al’ummar jihar da su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum domin jihar ta ci gaba da zaman lafiya

 

Sanarwar ta kara da cewa gwamnatin za ta ci gaba da sanya ido kan lamarin domin tunkarar duk wani mutum ko bangarorin da ke kokarin kawo cikas ga zaman lafiya da jihar.

 

Tun da farko dai wata babbar kotun tarayya da ke Kano ta bayar da umarnin korar Sarki Muhammadu Sanusi II daga fadar Kofar Kudu, yayin da wata babbar kotun jihar ta hana ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro aiwatar da umarnin korar.

 

A ranar Talata ne kotun tarayya ta umurci ‘yan sanda da su tabbatar da duk wani hakki da alfarmar da ya kamata a ba wa Sarkin Kano na 15, Aminu Bayero a matsayin hakki na Sarkin Kano.

 

Alkalin kotun, Mai shari’a S. A. Amobeda, wanda ya bayar da umarnin tsohon bangaren, ya bayyana cewa an yi wannan umarni ne domin tabbatar da adalci da kuma wanzar da zaman lafiya a jihar Kano.

 

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: