Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan ta Kasa Olumuyiwa Adejobi ya bayyana cewa rundunar ba za ta iya kama ‘yan bindigan da ke sanya bidiyon nuna kudin fansar da suka karba a daga hunnun mutane ba a shafukan sada zumunta a lokaci daya.

Kakakin ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X a jiya Juma’a.
Adejobi ya ce rundunar ƴan sandan na iya bakin ƙoƙarinta wajen kama mutanen, amma rundunar ba za ta iya kamasu a lokaci guda ba.

Kakakin na wannan kalami ne bayan wani hoto da masani kan sha’anin tsaro Zagazola Makama ya sanya a shafinsa na X wanda ya ke nuna ƴan bindiga ɗauke da kuɗaden fansar da suka amsa daga hannun mutane.

A martaninsa kan hotunan da Zogazola ya sanya a shafinsa na X, Adejobi ya bayyana cewa jami’an tsaro na iyaka bakin ƙoƙarinsu wajen ganin sun an tabbatar da tsaro a fadin Najeriya.
A kalaman nasa Adejobi ya buƙaci al’ummar Kasar da su dunga yabawa ƙoƙarin jami’an tsaro wajen tabbatar da tsaro a Kasar.
Acewarsa a kowacce rana su na kama ‘yan ta’adda masu yawa, kuma kowanne daga cikinsu zai fuskanci hukunci.
Ya kara da cewa jami’an Soji da na ‘ƴan sanda na iya bakin kokarinsu,domin ganin an samu tabbataccen tsaro a fadin Kasar, don haka ya bukaci da mutanen sun dunga jinjinawa irin kokarinsu.
Adejobi ya kuma bukaci al’ummar Kasar da su hada kai da jami’an tsaro domin magance matsalar rashin tsaro da sauran laifuffukan da suka addabi Kasar.