Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) bangaren matasa a Jihar Taraba ta bayar da umarnin gudanar da azumi tare da addu’o’i na tsawon kwanaki uku domin samun sauki daga Allaha akan rashin ruwan sama da aka dade ba a yi ba a jihar .

Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar a yau Lahadi a Jihar.

Shugaban kungiyar matasan na CAN Ephesian Jesse ya bayyana cewa daukar matakin hakan ya zama dole domin gyara laifuffukan da aka aikatawa ubangiji.

Shugaban ya bukaci mutane da su fito domin yin addu’o’i da kuma azumi domin neman ruwan sama, sakamakon yadda amfanin gona ya fara lalacewa.

Matasan sun kuma bukaci al’ummar Kiristoci a Jihar su fara addu’o’in kafin daga bisani musulmai su yi azumi daga gobe Litinin.

Kungiya na wannan kiranne bayan rashin ruwan sama da Jihar ke fuskanta wanda hakan ya fara illata amfani gona a fadin Jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: