Gwamnan Jihar Kano Injiniya Abba Kabir ya nuna rashin jindadinsa akan yadda tsohon gwamnan Jihar Dr Abdullahi Umar Ganduje ya tafiyar da salon mulkin a lokacin yana jagorantar Jihar.

Gwamna Abba ya bayyana haka ne a yayin taron karawa juna sani na ma’aikatan Jihar kan cin hanci da rashawa a ranar Asabar.
Acewar gwamnan wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Comrd Aminu Abdulsalam Gwarzo ya ce a zamanin mulkin Ganduje Kano ta fuskanci mafi munin cin hanci da rashawa fiye da kowacce gwamnatin da ta jagoranci Jihar.

Gwamnan Abba ya kara da cewa Jihar Kano ta fi kowace jiha a Jihohin Kasar samun matsala akan cin hanci a lokacin mulkin Ganduje tun daga shekarar 2015 zuwa 2023 da ya kammala mulkin Jihar.

Kazalika gwamna Abba ya ce cin hanci da rashawa na matukar kawowa kasa Cikas da kuma dakile ci gabanta.
Acewarsa a yankin Arewa maso Yamma Jihar Kano tafi kowacce Jiha shiga matsala musamman akan cin hanci da rashawa.
Gwamna Abba ya bayyana cewa kadarorin jihar da dama an cefanar da su ba bisa ka’ida ba, ya yin da manyan ayyukan Jihar aka watsar da su wadanda na daga cikin matsaloli da suka fuskanta bayan karbar mulkinsu daga hannun Ganduje.
Gwamna Abba ya kara da cewa cin hancin da Jihar ta fuskanta a lokacin mulkin Ganduje ya nakasa Jihar musamman a bangaren samar da ruwan sha wanda ya jawo karancin ruwa a Jihar.
Ya ce hakan ya faru ne bayan karbar bashin Yuro miliyan 6 a bangaren domin kawo sauya.