Gwamnatin Tarayya ta dakatar da aikin wani bangare na hanyar Kano zuwa Maiduguri bisa yadda ‘yan kwangilar aikin titin suka dauki dogon lokaci ba su ci gaba da gudanar da aikin ba.

Ministan Ayyuka a Kasa Dave Umahi ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Orji Uchenna Orji a fitar a jiya Asabar.
Ministan ya kuma nuna damuwa akan yadda kamfanin yake gudanar da aikin, ya ce hakan zai kawowa ‘yan Najeriya masu amfani da hanyar cikas.

Minista ya kara da cewa ba za su zuba idanu su bar aikin yana tafiyar wahainiya ba wanda hakan kuma nakasu ne ga kasar.

Umahi ya ce masu bin hanyar na matukar shan wahala sakamakon gaza karasa aikin, inda ya ce gwamnatin tarayya karkashin Bola Tinubu tana duk mai yiwuwa wajen ganin ta inganta hanyoyin kasar.
Gwamnatin ta tarayya ta bayar da kwangilar ne ga kamfanin Dantata & Sawoe Ltd tun a shekarar 2007 wanda ake ta samun matsala akan aikin.