Ƙungiyar da ke rashin kare tattalin arzikin kasa SERAP ta yi kira ga shugaban Bola Tinubu da ya gudanar da bincike akan yadda gwamnonin Jihohin Kasar 36 da kuma birnin tarayya Abuja suka yi amfani da bashin da suka karɓo daga bankin duniya.

Kungiyar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun mataimakin daraktanta Kolawale Oluwadare ya ta fitar a yau Lahadi.
SERAP ta bukaci shugabaTinubu da ya umarci ministan shari’a na Kasa Lateef Fagbemi SAN da hukumomin da ke yaƙi da cin hanci da rashawa na EFCC da ICPC da su gaggauta bincikar yadda aka kashe bashin dala biliyan 1.5 da suka karba daga bankin duniya.

Kungiyar na kiran ne bayan gwamnonin Kasar sun ciyo bashin daga bankin na duniya domin rage raɗaɗin talauci da kuma ƙara inganta jin daɗin al’ummar Jihohinnasu.

A sanarwar SERAP ta kuma sake buƙaci shugaba Tinubu da ya umurci Ministan na shari’a da hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa da su gaggauta bincikar zargin badakalar bashin dala biliyan 3.121 da gwamnatin tarayya ta karɓo daga kasar China.
Wasu rahotannin sun bayyana cewa bashin dala biliyan 1.5 da bankin duniya ya bai’wa ilahirin Jihohin Kasar da baban birnin kasar Abuja da kuma bashin dala biliyan 3.1 da gwamnatin tarayya ta samu daga China an karkatar da su ta wata hanyar ba tare da ansan yadda aka yi da su ba.
SERAP ta ce bincike tare da tuhumar zargin cin hanci kan almundahanar da bashin na bankin duniya da na China suka bayar zai yi daidai da kundin tsarin mulkin Najeriya.
Kungiyar ta ce kowanne gwamna a lokacin da ya ke kan kujerarsa yana da kariya daga kamu ko tuhuma, amma kuma bashi da kariya daga bincikensa har zuwa lokacin da zai sauka daga mukaminsa lokacin da bashi da kariya.
Kungiyar ta SERAP ta kuma bai’wa Shugaba Tinubu wa’adin mako guda domin daukar matakin da ya kamata.
SERAP ta ce matukar shugaban bai yi wani abinda ya dace ba har lokacin karewar wa’adin ta ce za ta ɗaukar matakin shari’a akan hakan.