Shugaban hukumar karbar korafe-korafen jama’a da yaki da rashawa a Kano Muhuyi Magaji Rimingado ya bayyana cewa ‘yan siyasa na amfani da ma’aikatan gwamnatin jihar wajen satar kudaden al’ummar Jihar.

Muhuyi ya bayyana hakan ne a yayin wani taron karawa juna sani da hukumarsu ta PCACC ta shirya tare da hadin guiwar ofishin shugaban ma’aikatan Kano karkashin shirin (ROLAC II).
A yayin taron Rimingado ya ce ya zuwa yanzu hukumar ta su ta bankaɗo Naira biliyan 18 da wasu ‘yan siyasa suka yi sama da fadi da ita ta hanyar amfani da wasu ma’aikatan Jihar.

Shugaban ya ce sun shirya taron ne don fadakar da ma’aikatan Jihar bayan ganowar da sukai ma’aikatan da laifin karbar rashawa domin gujewa rudin ‘yan siyasa masu karbar rashawa.

Muhuyi ya kara da cewa kaso 90 na rashawa da ake yi a Jihar na faruwa ne a yayin da ‘yan siyasar za su sayi kayayyaki, inda a lokacin ake hada baki da ma’aikata ake karkatar da kudaden.
Rimingado ya ce shirya irin wanna taron zai fadakar da ma’aikatan gwamnati akan dokokin da suka shafi siyo kayayyaki tare da tafiyar da kudin gwamnati.
Shugaban hukumar ya ce za su ilimantar da ma’aikatan akan yadda za su tafiyar da kudin jihar ta Kano tare da kiyaye hanyoyi da dokokin yaki da cin hanci da rashawa a lokacin gudanar da ayyukansu.
Kazalika Muhuyi ya ce a yayin taron sun hada da ma’aikatan kananan hukumomi bisa cewar suma ‘yan siyasa na amfani da su wajen satar kudin jama’a.
Break