Al’ummar garin Tulla da ke cikin karamar hukumar Buji a Jihar Jigawa sun wayi gari da jimami bayan wasu yara mata uku sun nutse a cikin ruwa.

Wasu shaidun gani da ido sun ce wadanda lamarin ya shafa Fatima Sule mai shekaru, 12 Nasiya Sale itama mai shekaru 12, da kuma Huwaila Sa’adu mai shekaru 13 sun nutse a ruwan ne a lokacin da suke yankar ciyawa a kusa da wani kogi domin ciyar da dabbobinsu.

Sai dai bayan faruwar lamarin an yi kokarin ceto yaran amma ba a yi nasara ba har suka rasa rayukansu.
Mai magana da yawun Hukumar NSCDC na Jihar ta Jigawa Badruddeen Tijjani Muhammad ya ce hukumarsu ta samu kiran agajin gaggawa domin ceto yaran.

Jami’in hukumar ta NSCDC a karamar hukumar Buji Abdulrashid Suleiman Adam ne ya jagoranci aikin ceton yaran tare da kai su asibiti bayan daukosu.

Afkuwar lamarin ya haifar da tashin hankulan al’ummar ƙauyen, inda mutane da dama suka fara mika ta’aziyyarsu ga ‘yan uwan yaran.

Sannan itama hukumar NSCDC ta jajanta wa iyayen yaran da suka rasa rayukannasu.
Hukumar ta ce tana ci gaba da bincike domin gano yadda lamarin ya faru ga yaran.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: