Gwamnatin Jihar Kano ta cire dokar hana fita da ta sanya a Jihar a yayin zanga-zangar da aka gudanar kan tsadar rayuwa da ake fuskanta a Kasar.

Gwamnatin ta cire dokar ne baki dayan ta a yammacin yau Litinin ta cikin wata sanarwa kwamishinan yada labarai Baba Halilu Dantiye ya fitar.

Kwamishinan ya ce gwamnan Jihar Injiniya Abba Kabir Yusuf ne ya bayar da umarnin cire dokar baki dayan ta duba da yadda al’amura suka daidaita a fadin jihar.

Kwamishinan ya kuma buƙaci al’ummar Jihar da su ci gaba da kasancewa masu bin doka da oda a Jihar.

Dantiye ya kuma roƙi al’ummar Jihar da su yiwa Jihar addu’a domin samun dawamammen zaman lafiya da kuma ƙasa baki ɗaya.

Tun da fari gwamnatin ta sanya dokar ne a ranar 1 ga watan Augustan da muke ciki bayan fara zanga-zangar lumana da aka yi kan tsadar rayuwa daga bisani kuma ta rikide zuwa tarzoma a Jihar.

Hakan ya sanya gwamnatin ta sanya dokar tsawo sa’o’i 24, daga bisani ta sassauta daga karfe 8 na safiya zuwa karfe biyu na 2 na rana, ya yin da akarshe ta mayar da dokar daga karfe 6 na safiya zuwa karfe 6 na yamma.

Leave a Reply

%d bloggers like this: