Shugaban Kasa Bola Tinubu ya rantsar da sabuwar shugabar ma’aikata ta tarayya Misis Didi Esther Walson-Jack.

Shugaban ya rantsar da ita ne a yau Litinin a yayin taron majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) wanda ya jagoranta, tare kuma da yin bankwana da shugabar ma’aikatan Dr Folasade Esan wadda wa’adin ta ya kare a yau.
A yayin jawabinsa a lokacin rantsarwar, gabanin fara taron na FEC shugaban ya bayyana cewa Didi Walson-Jack cewa za ta dora daga inda Misis Esan ta tsaya.

Tinubu ya kuma yi addu’ar Allah ya riko da hannayen sabuwar shugabar ma’aikatan a lokacin gudanar da ayyukanta.

Kafin rantsar da ita shugaba Tinubu ya amince da nadin Walson ne tun a ranar 17 ga Yuli shekarar nan.