Aƙalla mutane uku ake zargi sun rasa rayuwarsu yayin da gidaje sama da 1,000 su ka rushe a jihar Bauchi.

Hakan ya faru ne sakamakon ambaliyar ruwan sama da aka samu a jihar.


Hukumar bayar da agajin gaggawa a jihar SEMA ce a tabbatar da mutuwar mutanen wanda ta ce an samu rushewar gine-gine da dama.
Jami’an hukumar sun ziyarci ƙananan hukumomin Shira, Giade, Karagun.
Shugaban hukumar ya ce mutane uku da su ka mutu yan ƙaramar hukumar Shira ne.
A cewarsa, da yawa daga mutanen karamar hukumar Katagun sun bar gidajensu sakamakon ambaliyar ruwan.
Tuni gwamnatin jihar ta ki kayan tallafi wanda su ka haɗa da masara, shinkafa, da tabarmi.
Sakataren gwamnatin jihar Ibrahim Kashim ne ya kai kayan a madadin gwamnan jihar.
Dangane da gadar Bauchi zuwa Kano wadda ruwa ya lalata, gwamnatin ta ce za a kammala aikin ba da jimawa ba.