Majalisar tsaffin shugaban ƙasa a Najeriya ta yaba da tsarin tafiyar da mulkin shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Hakan na zuwa ne yayin da shugaba Bola Tinubu ya jagoranci zaman na farko a yau tun bayan kasancewarsa shugaban Najeriya.


Tsaffin shugaban Najeriya Goodluck Jonathan da Muhammadu Buhari ne su ka halarta.
Yayin da tsaffin shugaban ƙasa Yakubu Gawon da Abdussalam Abubakar su ka halarta ta intanet.
Zaman ya samu halartar mashawarcin shugaban ƙasa kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu wanda ya yi bayani danane da zanga-zangar yunwa da aka yi a ƙasar a baya bayan nan.
Haka kuma wasu daga cikin ministoci sun halarta da shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa.
Manufar zaman ita ce bayar da shawarwari dangane da tsarin tafiyar da gwamnatin kasar.
Wannan dai shi ne karo na farko da shugaba Tinubu ya jagoranta.