Rundunar ‘yan sanadn Jihar Sokoto ta musanta jita-jitar yin garkuwa da mutane 150 yankin Sabon birni da sauran wasu yankuna a Jihar, bayan hallaka sarkin Gobir Alhaji Isa Bawa.

Jam’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Jihar Ahmad Rufa’i ya musanta zargin, ya ce rundunar su ba ta da masaniya akan sace mutanen.
Rufa’i ya kara da cewa rundunar su ta na tabbatar da dukkan hare-hare da aka samu a jihar ne ta hanyar kai mata rahoton faruwar hakan a hukumance.

Acewarsa matukar ba a kai’wa rundunar rahoton farin wani lamari ba, to babu abinda za ta iya cewa akan hakan.

Kakakin ya ce amma yankin na karamar hukumar Sabon birnin da kuma yankin Sokoto ta Gabas, yankuna su na fama da matasalar rashin tsaro.
Rufa’i ya kara da cewa mafiya yawa daga cikin mazauna yankin na tsoron gayawa jami’an tsaro al’amuran da ke faruwa a yankin, saboda tsoron ‘yan ta’addan.
Kakakin ya ce rashin bai’wa jami’an tsaro rahoton abubuwan da ke faruwa a yankin ne ke kara ta’azzara matsalar rashin tsaro a yankunan.