Gwamnan Jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya bayar da izini rufe dukkan asusun bankuna na ma’aikatu da hukumomin Jihar.

Babban hadimin gwamnan kan kafafen yada labarai Hassan Sani Tukur ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X a yau Laraba.
Sanarwar ta ce gwamnan ya bayar da umarnin rufe dukkan asusun ajiyar ma’aikatun da hukumomin ne domin ta canza tsarin yadda za ta dunga karba, da ajiyewa da kuma rarraba kudaden a Jihar.

Tukur ya ce matakin na gwamnan na daga cikin tsare-tsare gwamnatin Jihar na komawa amfani da Asusun bai daya da hukumomi da ma’aikatun Jihar.
