Hedkwatar tsaro ta kasa ta ce jami’anta sun janye daga yankunan da ake fama da matsalar rashin tsaro a Jihar ne, bisa wasu shirye-shirye da suke karayi na tunkarar ‘yan ta’adda a yankunan.

Mai magana da yawun rundunar Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana hakan a jiya Talata a yayin wata fira da jaridar Punch.

Buba ya bayyana cewa hedkwatar ta janye jami’an sojin ta daga guraren ne tun a cikin watan Afrilun da ya gabata, duba da yadda ‘yan ta’addan suka yiwa jami’an kwanton bauna.

Ya kara da cewa jami’ansu da dama sun rasa rayukansu, tare da kayan aiki, bayan taka bama-bamai da suka yi wadanda ‘yan ta’addan suke binnewa.

Acewar Buba maharan na amfani ne da rashin kyan hanyoyin, wajen yiwa jami’annsu kwanton bauna.

Edwad Buba ya ce an janye jami’an ne na wucin gadi, kuma nan bada dadewa jami’an za su koma yankunan, bayan gama gano yadda za su tunkari maharan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: