Majalisar dattawa a Najeriya ta tantance sabbin ministocin da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa a makon da ya gabata

Majalisar ta tantance ministocin ne a yau.
Daga cikin ministocin har da na jin kai da karamin ministan harkokin ƙasashen waje sai ministan ƙwadago.

Sauran su ne ministan ciniki da masana’antu z sai ministan harkokin kiwo da ƙaramin ministan gidaje

Haka kuma akwai ƙaramar ministan ilimi.
Majalisar ta so tantance ministocin a jiya kamar yadda Bashir Garba Lado mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan sha’anin majalisa ya sanar, sai dai daga bisani aka daaga zuwa yau Laraba.
Shugaba Tinubu ya sauyawa wasu ministoci wurin aiki, yayin da ya sallami wasu tare da naɗa wasu.
Shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio ya hori sabbin ministocin da su kasance masu bayar da gudunmawar wajen tabbatar da tsarin shugaban ƙasa naa Renew Hope.