Rundunar yan sanda a Abuja ta kama wata mota dauke da yara 59 da ake yunkurin safararsu.

 

Yan sandan sun ce yaran dukkanninsu yan ƙasa da shekara 12 a duniya ne.

 

An kama motar ne ranar Litinin wadda ake zargi an dakko yaran ne daga Kano.

 

Mutane biyu aka kama da zargin daukar yaran a cikin motar.

 

Daga ciki akwai direban mai suna Ali Ibrahim da kuma wani Alhassan Ibrahim

 

Da yake gabatarda su ga yan jarida, kwakishinan yan sanda a Abuja Tunji Disu ya ce a bincken da su ka fara yi sun gano cewar an dauki yaran ne daga Kano da nufin kai su jihar Nassarawa.

 

A cewar sa direban, ya dauki yaran ne da nufin kai su jihar Nassarawa domin basu horo.

 

Sai dai jami’an sun zargesu da safarar yara da kuma cin zarafinsu da take hakkinsu.

 

Kwamishinan ya bukaci iyaye da su dinga sa ido a kan yayansu domin kare yancin su.

 

Sannan ya ce za a tabbatar an mika yaran ga iyayensu tare da gurfanar da dukkan wadanda ake zargi da hannu a gaban kotu domin girbar abinda su ka shuka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: