Gamayyar gwamnonin Kudu maso yammacin Najeriya na shirin yin aikin hadin gwiwa da nufin yakar mayakan ISWAP.

Kungiyar gwamnonin za su dakile yukurin kafa sansanin mayakan ISWAP a shiyyarsu
Gwamnonin jihohin Legas, Ogun, Oyo da Osun da Ekiti sai Ondo ne su ka haɗa kai da nufin hana yaduwar kungiyar.

Za su samar da jami’an hadin gwiwa da za au daƙile wanzuwar mayakan a yankin

Hakan na zuwa ne bayan zaman da gwamnonin su ka y jiya Alhamis a gidan gwamnatin jihar Legas.
Kuma sun dauki matakin haka ne bayan da su ka samu labarin wasu daga mayakan sun fara zuwa wasu dazukan yankin
A watan Janairu gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde ya gargadi yan ta’addan da ke tserewa daga arewacin kasar zuwa jihar sa.
A jihar Osun kuwa jami’an tsaron DSS sun kama wasu mutane goma da ake zargi mayakan Iswap ne.
Shugaban kungiyar gwamnonin kuma gwamnan jihar Legas Babajide Sawo Olu ya ce kungiyar ta amince da aikin hadin gwiwa don dakile yunkurin mayakan.
Sannan za su yi amfani da dabaru daban daban don ganin an bai wa yankunan tsaro yadda ya kamata.