Gwamnatin Tarayya ta mayar da martani ga kalaman shugaban sashin kula da laifukan da su ka shafi kuɗi na a babbar kasuwar hada-hadar kuɗaɗen yanar gizo ta Binance wato Tigran Gambaryan, na zargin cewa ƴan majalisar wakilan Najeriya guda uku sun buƙaci cin hancin Dala miliyan 150 daga wajensa.

A wata wallafa da ya fitar jiya Juma’a Gambaryan wanda ya shafe watanni takwas a tsare a Najeriya bisa zargin cin hanci da rashawa, ya bayyana sunayen Philip Agbese, Ginger Onwusibe da kuma Peter Akpanke dukkaninsu ƴan majalissun tarayya, a matsayin mutanen da suƙa buƙaci ya basu maƙudan kuɗaɗen.

Sai dai jami’in na Binance, ya gaza bayar da wata ƙwaƙƙwarar hujja, wacce za ta tabbatar da zargin nasa.

Ya kuma ce hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta shiga maganar ta su da majalisar wakilan, inda su ka haɗu da su a ofishinsu ranar 5 ga watan Janairun 2024, sai dai sun yarda da cewa dole sai mun bi duk wani abu da ƴan majalisar wakilan suka umarce mu.

Yayin mayar da martani ga kalaman, ministan yaɗa labarai da wayar da kan ƴan ƙasa Mohammed Idris a cikin wani jawabi, ya buƙaci al’umma da su yi watsi da ikirarin zarge-zargen marasa tushe.

Idris ya ƙara da cewa duk da cewa gwamnatin tarayya tana bi a sannu a lamarin Gambaryan, kuma ta na bin manyan matakan diplomasiyya dan warware matsalar, amman ya zama wajibi a gare su dakatar da zantukansa marasa tushen gaskiya dan kar su ci gaba da yaɗuwa.

Ministan ya ƙara da cewa, sun musanta duk wasu kalaman mayar da martani da Gambaryan ya yi akan hukumomin Najeriya, kuma su na buƙatar ƴan ƙasa da su yi watsi da su, saboda basu da tushe balle makama.

Ya ce abu ne mai muhimmancin gaske a fuskanci cewa ba wai iya rashin hujja zarge-zargen su ke da shi ba, har da rashin sahihanci. Ƙoƙari ne kawai na sa don ganin ɓatawa ƴan majalissun da su ka dage sai ya fuskanci hukunci suna.

Leave a Reply

%d bloggers like this: