Karamin Ministan tsaro Muhammad Bello Matawalle ya bayyana cewa ya zama wajibi gwamnatin Tarayya ta dauki mataki mai karfi akan kasar Canada bisa hana hafson tsaron Kasar nan Janar Christopher Musa da wasu manyan jami’an sojin Najeriya bizar shiga Kasar.

A wata wallafa da Ma’aikatar tsaro ta fitar ta bayyana cewa hana Christopher Musa da sauron sojojin Najeriya shiga Kasar ta Canada, babban cin zarafi ne da kuma raini ga Najeriya.

Sannan Matawalle ya bayyana cewa hakan na iya kawo cikas ga dangantakar da ke tsakanin Kasashen biyu.

Acewar sanarwar ya zama wajibi a gudanar da bincike akan dalilan Kasar ta Canada na hana manyan jami’an sojin Najeriya shiga Kasar ta bayan gayyatarsu da aka yi zuwa wajen taron girmama tsofaffin jami’an soji.

Matawalle ya kara da cewa dole ne Kasar ta Canada ta fito ta bayyana dalilinta wanda za a gamsu dashi akan matakin da ta dauka na hana Jami’an sojin na Najeriya shiga cikinta, ko kuma Najeriya ta dauki matakin diflomasiyya mai tsauri.

Leave a Reply

%d bloggers like this: