Tsohon shugaban ƙasar Najeriya Goodluck Ebele Jonathan ya buƙaci shugabannin yankin nahiyar Afirka, da su ɗauki matasan yankin a matsayin kadara da za a iya dogaro da ita a fannoni daban-daban na ci gaba, ba wai a matsayin nauyi gare su ba.

Jonathan ya bayyana hakan ne jiya Asabar cikin wani jawabi ta hannun mai magana da yawunsa Eze Ikechukwu, tare da kira ga yin abinda ya dace da zai yi tasiri mai kyau ga rayuwar matasan.
Wannan ya biyo bayan wani tsokaci na musamman a birnin Addis Ababan Ƙasar Ethiopia, yayin ƙaddamar da wani rahoto akan ci gaban ƙasashen Burkina Faso, Guinea, Gabon, Mali da Nijar.

Jonathan ya buƙaci ƙasashen Afirka da su sanya kuɗi a ɓangaren ilimi, ci gaban zamani, da kuma bunƙasa sana’o’i, dan fito da zaƙwaƙurancin matasan nahiyar da yin gogayya da takwarorinsu na duniya da fannin shugabanci.

Ya kuma bayyana cewa sanya kuɗaɗen a waɗannan ɓangarorin ba zaɓi bane, ya zama wajibi ne dan ci gaban nahiyar Afirka a gobe da kuma tsayawa da ƙafarta.
Goodluck ya bayyana yankin na nahiyar Afirka na fuskantar ƙalubale a fannonin jagoranci, raunin siyasa, mashashsharar tattalin arziƙi da kuma sauran tarin matsaloli.
Inda ya buƙaci shugabannin nahiyar da su fifita shigo da kowa da bunƙasa tattalin arziki, dan tabbatar da kyakkyawan tsarin siyasa da ci gaba mai ɗorewa a yankin.