Gwamnan jihar Filato Caleb Mutfwang ya dakatar da aikin haƙar ma’adanai a jihar, dan shawo kan matsalolin tsaro da su ka addabi jihar.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata dokar iko mai lamba 001 ta shekarar 2025, da aka bayyana wa manema labarai a yau Asabar a birnin Jos ɗin jihar ta Filato.

 

Gwamnan ya bayyana cewa ɗaukar mataki ya zama wajibi, sakamakon ƙarin samun matsalolin tsaro a yankunan da ake yin aikin haƙar ma’adanan a faɗin jihar.

Ya kuma ƙara da cewa hakan wani mataki ne game da yawan ayyukan haƙar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a jihar, waɗanda suka ta’azzara rashin tsaro, da kuma yawaitar shigowar masu haƙar ma’adanai baƙin haure ba bisa doka ba.

Mutfwang ya ce hakan ya janyo ƙaruwar ayyukan laifi kamar ta’addanci, garkuwa da mutane, safarar miyagun ƙwayoyi da kuma mallakar haramtattun makamai.

Gwamnan ya kuma ƙara da cewa wannan sabuwar dokar ta fara aiki ne tun daga jiya Juma’a, 21 ga watan Fabarairun shekarar 2025.

Gwamna Caleb ya kuma samar da kwamitin gyara da saisaita harkokin haƙar ma’adanan, wanda Kwamishinan shari’a na jihar Philemon Dafi zai jagoranta, dan tabbatar da aiwatar da gyararrakin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: